13 Mayu 2026 - 21:59
Source: ABNA24
Hizbulah Ta Kai Manyan Hare-Hare Arewacin Falasdinu

A mummunan harin jirage marasa matuki da Hizbullah ta  kai arewacin Falasdinu da aka mamaye jami'an Sahayoniya biyu suka jikkata

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar Ibrananci "Jerusalem Post" ta nakalto wata majiyar tsaro cewa Hizbullah ta kai mafi ƙarfin harin ta na jirage marasa matuki a jiya kan arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Wannan majiya ta bayyana cewa a yayin harin jiragen marasa matuki na Hizbullah, jami'an Sahayoniya biyu sun jikkata, kuma a wani hari na daban an samu gobara a wani sansanin soji a arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Hizbullah kimanin awa daya bayan guguwar farko ta hare-hare, ta harba wasu jirage marasa matuki da dama zuwa ga wannan sansani a arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Majiyar tsaro ta kuma jaddada cewa Hizbullah a jiya ta aiwatar da wani hari na jirage marasa matuki wanda aka tsara, wanda a fannin faɗi da yadda aka aiwatar da shi, shi ne hari na farko irinsa a kan arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Your Comment

You are replying to: .
captcha